Sanata Kwankwaso ya amsa sammacin fadar shugaban kasa, ya gana da Osinbajo

Sanata Kwankwaso ya amsa sammacin fadar shugaban kasa, ya gana da Osinbajo

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yau Litinin, 29 ga watan Junairu, 2018 a fadar shugaban kasa.

Zaku tuna cewa fadar shugaban kasa ta sammaci sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje akan adawar da suke yi tsakanin juna musamman kan batun taron da Kwankwaso ya shirya yi a Kano gobe Talata, 30 ga watan Junairu, 2018.

KU KARANTA: Kwankwaso ya jingine ziyarar da zai kai jihar Kano

Kafin ganawarsu, sanata Kwankwasi ya jingine zauwansa Kano bayan shawarwari da nasiha daga mutanen arziki kan tsoron rikicin da zai faru inda ya gudanar da taron.

Sanata Kwankwaso ya amsa sammacin fadar shugaban kasa, ya gana da Osinbajo
Sanata Kwankwaso ya amsa sammacin fadar shugaban kasa, ya gana da Osinbajo

Zaku tuna cewa kwamishinan 'yan sanda a jihar kano, CP Rabi'u Yusuf, ya shawarci Kwankwaso da ya janye ziyarar har sai hukumar ta gamsu cewar zuwansa ba zai haddasa rikici ba, shawarar da magoya bayan Kwankwaso su ka saka kafa suka shure ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng