Farashin gangar ‘danyen man fetur din Najeriya haura Dala $70
- ‘Danyan man fetur din Najeriya ya kara kasuwa yanzu a Duniya
- Kasashe masu arzikin fetur sun rage yawan abin da su ke hakowa
- Hakan na iya sa farashin litar man fetur ya kara tsada a Najeriya
Mu na samun labari cewa yanzu haka ‘Danyen man Najeriya ya kara kasuwa a Duniya inda gangar danyen man ya haura sama da Dala 70 a farkon wannan makon inji Jaridar Daily Trust ta kasar nan.
Farashin ‘danyan man fetur din ya kara kudi ne bayan da Kungiyar OPEC na Kasashe masu fitar da ke fitar da man fetur da irin su Rasha su ka rage adadin man fetur din da su ke hakowa a rana. A yau dinnan ne farashin man ya karu.
KU KARANTA: Shugaban Kasa Buhari ya gana da Gwamna Ortom
A karshen makon jiya dai danyan man na Najeriya watau Brent ya kara kudi ne zuwa Dala 70.05 a farkon makon nan yayin da man Amurka ya ke kan Dala 64.77. A farkon wannan watan ne Kasashen da ke da arziki su ka rage hako mai.
Rikicin siyasar Duniya na cikin abin da ya sa man ya tashi a Duniya. Sai dai hakan na iya zama matsala a gida Najeriya don kuwa ba mamaki farashin man fetur ya kara kudi daga N145 bayan tashin sa a Duniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng