Labari da Duminsa: Anyi jina-jina a sabon rikici tsakanin 'yan Gandujiyya da 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano

Labari da Duminsa: Anyi jina-jina a sabon rikici tsakanin 'yan Gandujiyya da 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano

- Rikice ya barke tsakanin 'yan Kwankwasiyya da 'yan Gandujiyya

- Wasu samu rauni sakamakon rikicin

- Rikicin ba zai rasa nasaba da batun ziyarar da Kwankwaso zai kai Kano ba karshen wata

Rahotanni da muke samu daga jihar Kano na nuni cewar an barke da rikici tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso; 'yan Kwankwasiyya, da magoya bayan gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje; 'yan Gandujiyya.

Wata majiya ta shaida mana cewar mogoya bayan Gandujiyya ne suka kai wa 'yan Kwankwasiyya hari tare da raunata masu magoya baya. Saidai bamu da tabbacin hakan shine takamaiman abinda ya faru.

Labari da Duminsa: Anyi jina-jina a sabon rikici tsakanin 'yan Gandujiyya da 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano

Ganduje da Kwankwaso

A cikin rahoton da muka samu, mun ga wani dan Kwankwasiyya, Walid Abbas Sanusi (Walidin Kwankwasiyya) cikin jini. Walid dan uwa ne ga Abdullahi Abbas, jigo a tafiyar Gandujiyya.

Kazalika rahoton da muka samu bai ambaci inda rikicin ya faru ba, illa iyaka dai an bayyana cewar a cikin garin Kano abin ya faru.

DUBA WANNAN: Tsuguni bata kare ba: Wani sabon rikici tsakanin Hausawa da wasu matasa ya kara barkewa a jihar Benuwe

An dade ana takun saka tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da na Gandujiyya a jihar Kano.

Ki a cikin satin da ya wuce saida kafafen watsa labarai suka wallafa wani faifan bidiyo dake nuna Abdullahi Abbas, jigo a jam'iyyar tafiyar Gandujiyya, na ambaton cewar zasu jefi Shaidan idan ya shigo jihar Kano. Kalaman da jama'a suka fassara yana nufin Kwankwaso ne.

Kwankwaso zai kai ziyara jihar Kano a karshen watannan da muke ciki domin yakin neman zabe ga magoya bayansa a zabukan kananan hukumomi da za'a yi a jihar watan Fabrairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel