Hukumar NSCDC ta kama man fetir lita 1000 daga hannun masu siyar wa 'yan ta'adda

Hukumar NSCDC ta kama man fetir lita 1000 daga hannun masu siyar wa 'yan ta'adda

- Hukumar tsaro na NSCDC tayi nasarar kwace lita 1000 na man fetir daga masu sayar wa 'yan Boko Haram

- Masu sayar da man fetir din su tsere ne sun ban jarkunan man fetir din da suka boye cikin buhuna a babban titin Dikwa bayan sun hangi motar rundunar

- Jami'an rundunar kuma sun gano kayan masarufi kamar sabulu, man shafawa, sukari, gari, tabbar sigari da sauran su cikin kayan da miyagun suka bari

Hukumar tsaro na Nigeria Security and Civil Defense Corp (NSCDC) reshen jihar Borno tace ta kama man fetir misalin lita 1000 daga wasu 'yan kasuwa da ake zargin suna sayar da man fetir din ka gan 'yan Boko Haram.

Jami'an NSCDC sun kama masu sayar wa 'yan Boko Haram man fetir
Jami'an NSCDC sun kama masu sayar wa 'yan Boko Haram man fetir

Kwamandan rundunar, Mista Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a garin Maiduguri, ranar Laraba a wata hira da hukumar dillanci labarai na kasa (NAN). Ya cigaba da cewa sashin yaki da masu bannata kayan gwamnati ne sukayi kacibus da masu man yayin da suke zagaye a garin Ngom da ke karamar hukumar Mafa na jihar ta Borno.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace wani basarake a kudancin jihar Kaduna

Yace masu sayar da man su ranta a na kare bayan sun hango motar hukumar ta NSCDC a babban titin Mafa zuwa Dikwa, man fetir din da ke cikin jarkoki guda 49 an boye su ne cikin buhuna.

Jami'an na NSCDC kuma sun gano kayan abinci da na masarufi da suka hada da sabulu, man shafawa, sukari, gari, tabbar sigari da kuma dunkulen maggi. Duk dai kayayakin an boye su ne domin kada jami'an tsaro su gano.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama wasu mutune biyu tare da jarkoki 30 na man fetur da kuma wasu jarkoki 6 na man fetur din daga wasu yan kasuwar duk a garin Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: