Buhari ya taba furta cewa Kwankwaso ya dace da mulkin Najeriya

Buhari ya taba furta cewa Kwankwaso ya dace da mulkin Najeriya

Wani ‘Dan siyasa a Kasar nan mai suna Muhammad Yusuf wanda ya taba aiki da Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana abin da ke tsakanin Kwankwaso da Buhari da yadda Kwakwaso ya ceci rayuwar Buhari hannun ‘Yan ta’adda kwanakin baya.

Idan ba ku manta ba a 2013 an taba kai hari inda aka kusa ganin bayan Shugaba Buhari a Garin Kaduna. Muhamamd Yusuf wanda kusan dangin sa ‘Yan uwa ne wajen Shugaban Kasar ya bayyana cewa Kwankwaso ya ceci tsohon Shugaban a Ranar.

Buhari ya taba furta cewa Kwankwaso ya dace da mulkin Najeriya
Shugaban Kasa Buhari da 'Yan APC wajen yakin zabe

Yusuf yayi wannan rubutu ne kwanakin baya a Jaridar The Cable inda yace jim kadan bayan abin ya faru Shugaba Buhari ya kira Kwankwaso a waya inda yayi masa godiya. Gwamnan Kano a lokacin ne ya mikawa Shugaban Kasar kyautar motar da yake ciki.

KU KARANTA: Kataborar Buhari ya nuna Gwamnatin APC ba ta da fasali Inji PDP

Abin dai ya zo da sauki don kuwa harsashi ba ya ratsa motar, ta haka ne Muhammadu Buhari ya tsira a wannan rana. Daga baya dai Rabiu Kwankwaso ya taka mota domin gaida Buhari bayan hadarin. Da dama dai ba su san abin da ya wakana ba a wancan lokaci.

A cewar Yusuf, wata rana Buhari ya taba cewa zai so ya ga Kwankwaso ya zama Shugaban Kasa lokacin da Nduke Obiegbuna na Jaridar This Day ya tamabaye sa wanda ya dace da mulkin Najeriya. Sa'an nan Buhari yace Kwankwaso zai iya gyara Najeriya cikin kankanin lokaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng