Lafiya uwar jiki: Illar shan gishiri sosai a jikin mutum
- Masana sun yi rubutu game da illar gishiri da yawa ga mutum
- Akwai mutane 3 da sai sun bi a hankali wajen shan gishiri
- Yawan shan gishiri na kawo cutar hawan jini da na koda
Tun ba yau ba Masana sun yi rubutu game da illar kwankwadar gishiri da yawa a jikin mutum don haka ne mu ka kawo maku kadan daga ciki.
1. Hawan jini
Shan gishiri da yawa yana jawo hawan jini saboda sinadarin sodium na sa mutum ya rage bawali wanda rashin sa kan sa jinin mutum ya kara yawa har ta kai jinin ya hau sama.
KU KARANTA: Dan kunar bakin wake na karar Amurka a Kotu
2. Cutar stroke
Haka kuma yawan shan gishiri na kawo cutar ‘stroke’ wanda ka iya sa mutum ya yanke jiki ya fadi. Hawan jini ne dai ke kawo wannan a lokacin da zuciyar mutum ta buga.
3. Cuttukan koda
Yawan shan gishiri na kawo larurar koda saboda yawan sinadari na Sodium da ke cikin gishiri na iya kawo illa har ta kai mutum ya kamu da cutar osteoporosis.
Mutanen da su ka zarce shekaru 50 da masu cutar sukari da kuma masu hawan jini dole su bi a sannu wajen shan gishiri Inji masana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng