Dandalin Kannywood: Saura kadan in aure Nafisa Abdullahi amma na fasa - Adam Zango

Dandalin Kannywood: Saura kadan in aure Nafisa Abdullahi amma na fasa - Adam Zango

Fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood kuma jigo a harkar Adam A. Zango ya fito ya shaidawa duniya cewa ya shafe shekaru akalla uku kafin su bata kowa ya kama gaban sa.

Adam A. Zango dai wanda ake yi wa lakabi da yariman mawaka watau Prince da kuma yanzu haka yake da mata biyu na aure ya bayyana cewa sun tafka mahaukaciyar soyayya inda kuma har ta kai ga sun kusa yin aure amma sai kaddara ta riga fata.

Dandalin Kannywood: Saura kadan in aure Nafisa Abdullahi amma na fasa - Adam Zango
Dandalin Kannywood: Saura kadan in aure Nafisa Abdullahi amma na fasa - Adam Zango

KU KARANTA: Mijina ya bani shawarar in dawo sana'ar fim - Fati Ladan

Legit.ng dai ta samu cewa shahararren dan fim din kuma mawaki ya dai ki fitowa fili ya fadawa duniya meye musabbabin rabuwar ta su amma dai ya bayyana cewa kawai dai kaddara ce ta raba su kuma daman can Allah bai nufi zata zama matar sa ba.

Idan mai karatu dai zai iya tunawa mun kawo maku wani rahoto a kwanan baya inda Nafisa Abdullahi din ta bayyana cewa ba zata auri dan fim ba kuma ta kusa yin auren.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng