Rundunar Soji tayi wa barayin shanu da tumaki diran mikiya

Rundunar Soji tayi wa barayin shanu da tumaki diran mikiya

- Rundunar Soji ta kai samame akan 'yan fashin shanu da tumaki da suke boye a dajin Kahiru da ke Jihar Zamfara

- Rundunar Sojin ta samu kashe daya daga cikin 'yan fashin a yayin da suran suka ranta a na kare

- Rundunar Sojin ta samu kubutar da shanu 50 da awaki 82 da tinkiyoyi 25 daga hannun 'yan fashin

A ranar Lilitini, 25 ga watan Satumba, da ya gabata ne Rundunar Soji ta kai wani samame akan wasu da ake zargi da fashin shanu da tumaki. Wadannan 'yan fashi suna boye ne a dajin Kahiru da ke karamar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

'Yan fashin sun fara barin wuta akan sojin yayin da suka fuskance su a yunkurin su na tserewa. A nan ne fa sojin suka mayar masu da martani har suka samu nasarar kashe daya daga cikin 'yan fashin.

Rundunar Soji tayi wa barayin shanu da tumaki diran mikiya
Rundunar Soji tayi wa barayin shanu da tumaki diran mikiya

Sauran 'yan fashin tuni dai suka ari takalmin kare don tsira da ran su. Sojin sun samu nasarar kubutar da shanaye 50 da awaki 82 da kuma tinkiyoyi 25 da 'yan fashin suka gudu suka bari.

DUBA WANNAN: Ku daina fatan Yaki: Wani tsohon soja yayi wa kabilar Ibo nasiha mai ratsa jiki

An samu wannan rahoto ne daga Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman wanda shine Daraktan gudanar da dangartaka tsakanin Soji da al'umma.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164