Gwamnatin Iran za ta halatta auren dandano domin rage barna

Gwamnatin Iran za ta halatta auren dandano domin rage barna

- Kasar Iran za ta shigo da auren mutu'a saboda yawan zinace-zinace

- Bincike ya nuna cewa ana tafka mugun barna a Kasar musamman matasa

- Auren dandano zai bada dama a rage fasikanci kafin ayi aure a Kasar

Mun samu labari daga Jaridar Daily Mail cewa ana kokarin kawo karshen kwanciya da maza kafin ayi aure a Kasar Iran.

Gwamnatin Iran za ta halatta auren dandano domin rage barna
Za a kawo karshen zinace-zinace a Iran

Gwamnatin Kasar Iran za ta halatta auren dandano domin a rage barna a Kasar domin kuwa bincike ya nuna kashi 80% na 'Yan matan kasar kan kwanta da wani kafin su yi aure. Kusan daya cikin biyar kuma na wannan kason kan bi 'Yan uwan su ne mata.

KU KARANTA: An ceto matan da su ka burma karuwanci

Auren dandano kan bada dama mutum ya sadu da wata na dan lokacin kafin a rabu. Wannan zai yi maganin zinace-zinacen da ake tafkawa a Kasar. Gidan labarai na Fox News yace tun yara mata su na kanana ake fara kwanciya da su. Mafi yawan mutanen kasar dai yara ne matasa.

Kwanaki kun ji cewa rashin Maza na aure a Najeriya na nema ya zama wani tashin hankali. Mazan aure su na matukar wahala a halin yanzu saboda jiran mai kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Meye abin duba kafin a fara soyayya?

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: