Kaf Kannywood ba mai kyan Fati Muhammad
Legit.ng ta ci karo da wani rahoto dake nuni ga cewa baá taba wata mace mai kyan Fati Muhammed ba a tarihin Kannywood.
Kamar ya dda kuka sani Fati Muhammed ta kasance fitaciyyar jarumar shirya fina-finan Hausa a lokutan baya.
A zamaninta ta kasance jaruma mafi shahara wacce ake ji da ita a harkar fim, saboda kwarewarta da kuma tsntsar kyawun da Allah ya yi mata.
A lokacin ita da jaruma Abida Muhammed ne suka kasance mata jarumai da ake ji dasu kuma mafi karantar shekaru.
![Kaf Kannywood ba mai kyan Fati Muhammad Kaf Kannywood ba mai kyan Fati Muhammad](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt57geoutg22i.jpeg?v=1)
Babu shakka mun tabbata da ace jarumann nan zasu dawo harkar fim a yanzu toh tabbass da zaá kara damawa da su.
KU KARANTA KUMA: Jigon APC a Kano ya sauya sheka zuwa PDP
Fati ta bar harkar fim ne bayan da tayi aure, wanda a lokacin mijin nata ma jarumin shirya fina-finai ne amma tafiyar batayi nisa ba suka rabu.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng