Hanyoyi 3 da amfani da citta ke tseratar da rayuwa

Hanyoyi 3 da amfani da citta ke tseratar da rayuwa

Binciken masana nazari a kan kiwon lafiya ya bayyana amfanin citta a jikin dan Adam

Tun shekaru sama da 4, 700, mutanen kasar Sin da Indiya su ke amfani da citta wajen magance cututtuka daban-daban. Citta tayi kaurin suna wajen amfani da ita cikin girki don sanya kanshi da dandano ga abinci kuma amfanin ta wajen kiwon lafiya ba zai musaltu ba.

Ga yadda hanyoyi uku na amfani da citta ke tseratar da rayuwar dan Adam

1. Bugu da cututtukan zuciya

Bincike ya nuna cewa idan aka yi amfani da citta tare da wasu kayan abinci irinsu tafarnuwa da albasa, su na hana daskarewar jini a jikin dan Adam wanda suke bunkasa karfin jini da zai rinka zagayawa a cikin tashoshin jini wanda hakan zai hana bugun zuciya da bayar da kariya wajen cututtukan zuciyar.

Hanyoyi 3 da amfanin citta ke tseratar da rayuwa
Hanyoyi 3 da amfanin citta ke tseratar da rayuwa

2. Rashin cin abinci da tashin zuciya

Amfani da citta bai tsaya wajen warkar da ciwon ciki kadai ba, don tun shekaru dubunnai da su gabata a ke amfani da ita wajen warkar da matsalar rashin cin abinci da tashin zuciya.

KU KARANTA: An yankewa wata mata daurin shekara 16 saboda ta tsiyayawa saurayin ta soyayyen mai

3. Rashin tacewar amfanin abinci a cikin ciki

Citta ta na inganta narkewarr abinci da wuri a cikin cikin dan Adam domin wasu nau'ukan abinci su na jimawa kafin su narke, bincike ya nuna cewa amfani da citta ya na habaka saurin narkewar abinci don idan abinci ya jima a cikin mutum bai narke sai ya lalace wanda hakan kan iya gadar da matsala ga lafiyar dan Adam.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel