Ashe jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq dan jarida ne?

Ashe jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq dan jarida ne?

Sani Sadiq ya kasance shaharen dan wasan fim din Hausa, daya daga cikin jaruman da ake damawa da su a harkar fim din Hausa. An haife shi a unguwar Gangare, karamar hukumar Arewacin Jos (Jos North) dake jihar Plateau a ranar 2 ga watan Fabrairu, shekara ta 1981.

Ya kammala karatun sa na firamare da sakandare a Gangare Jos. Daga nan, ya tafi jami’ar Jos, inda ya samu kwalinsa na difloma a karatun jarida. A 2004 Sadiq ya fara harkar fim. Ya zamo tauraro ne a shekara ta 2012.

Jarumin ya amshi lambar yabo a matsayin jarumin jarumai na Kannywood a shekarar 2012. Zuwa yanzu, ya fito a cikin fina-finai akalla guda 50. Sadiq na godiya ga Allah bisa nasarorin sa. Sadiq ya fito a fina-finai kamar su Maryam Diyana, Adamsy, da kuma Yan Uwan Juna. Da yake magana game da godiyarsa ga Allah da ya bashi aikin da ya daukaka shi, Sadiq ya ji dadin cewar ya yi karatu a garin Jos kafin ya shiga harkar fim.

Ashe jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq dan jarida ne?
Sadiq ya samu lambar yabo a matsayin jarumin jarumai akamfanin na shirya fina-finai Hoto: Dandalin Kannywood

Sadiq Sani na da kanne guda takwas, sannan kuma a yanzu haka ya na da mata da suke zaman aure mai inganci. A shafinmu, zaka san wasu abubuwa game da wannan jarumin mai tarin basira!

Ashe jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq dan jarida ne?
Sadiq Sani Sadiq da matarsa

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng