Dandalin Kannywood: Jarumi Adam Zango ya sa wata tsohuwa kuka

Dandalin Kannywood: Jarumi Adam Zango ya sa wata tsohuwa kuka

Jarumi Adam A Zango ya yi rabon kayan masarufi dama kudi agarin kaduna. mutane da yawa sun sami wannan kyauta ta kayan masarufi, abin burgewa da sha'awa shine, mafi yawan wadanda suka sami kyautar talakawane da kuma gajiyayyu da kuma marayu.

Acikin talakawan da suka sami kyautar harda wata tsohuwa, wanda take mazauniyar unguwar Zangon Kataf dake kaduna state. wanda sabida jin dadin abinda Adam A Zango ya yi mata har tana kuka.

Legit.ng ta samu labari daga wakilin majiyar mu Muhammed Lere ya zanta da ita ta sanar ma shi dalilin da yasa tayi kuka alokacin da aka bata kyautar Adam A Zango.

Dandalin Kannywood: Jarumi Adam Zango ya sa wata tsohuwa kuka
Dandalin Kannywood: Jarumi Adam Zango ya sa wata tsohuwa kuka

Acewar Tsuhuwar: "Wallahi bani da abinda zanci aranar, sai wata makociyata ta shigo tace ga yan fim can suna rabon kudi da kayan masarufi, nan fa na tashi da kyar. naje gurin sai naga Adamu dama kuma ya saba wannan rabon, yana zuwa kaina sai ya ba ni naira dubu dari biyu, wallahi ban san lokacin da nayi kuka ba dan murna." "Nagodewa Allah, Allah kare Adamu Allah Ya Kara Daukaka." Inji Tsohuwa Ladi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel