Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam

Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam

Ba yara kwai a lokacin da suke tasowa na da matukar amfani domin yana inganta girman jikin yaran saboda sinadarorin da kwan ke dauke da shi.

Legit.ng ta samu labarin cewa bayanai na kwararru ya nuna cewa kwai na dauke da sinadarorin Vitamin A, B12, D, B6 wanda ke taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki yara musamman ‘yan kasa da shekaru 5.

1. Dafaffen kwai na bude kwakwalwan yaro.

2. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin ‘lutein’ and ‘zeaxanthin’ wanda ke kara lafiyar idanuwar yaro.

3. Dafaffen kwai na kara karfin kashi a jikin yara kanana domin yana dauke da sinadarin Vitamin D.

Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam
Lafiya jari: Abubuwa 7 da cin kwai yake samarwa a jikin dan adam

4. Dafaffen kwai na dauke da sinadarorin leucine, phenylalanine, histidine, isoleucine, lycine, methionine, threonine, tryptophan da valine wanda suke taimakawa wajen gina jikin yaro da kuma kara masa jini.

5. Dafaffen kwai na kara girman kunba da gashin kan yara.

6. Omega-3 da ke cikin dafaffen kwai na taimakawa wajen bude kwakwalwar yaro kuma zai yi sauran gane abubuwa.

7. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin Iron da ke taimakawa wajen samar da issashen jini a jikin yaro Wanda rashin shi yakan sa aga yaro na kumbura.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng