Dandalin Kannywood: Shahararren mawaki Nura M. Inuwa zai angwance

Dandalin Kannywood: Shahararren mawaki Nura M. Inuwa zai angwance

- Kamar yanda muka sanar daku a wannan dandali cewa mawaki Nura M Inuwa zai angonce da amaryarsa yar garin katsina, to anan ana ci gaba da shagulgula kafin ranar dauren aure

- Amma da yake bikin na manyane kun san ba'a rasa 'yan kunji-kunji ataron biki

Kamar yanda muka sanar daku a wannan dandali cewa mawaki Nura M Inuwa zai angonce da amaryarsa yar garin katsina, to anan ana ci gaba da shagulgula kafin ranar dauren aure. Amma da yake bikin na manyane kun san ba'a rasa 'yan kunji-kunji ataron biki.

To shima bikin Nura ya tayar da zaune tsaye. Domin jarumai ne suke ta musayar yawu da fadi tashi akan yanda zasu birge jama'a a bikin Nura. duk wanda yake da budurwa a kannywood to wannan lokacin kudinsa sun shiga uku.

Legit.ng ta ruwaito cewa Adam A Zango yana daga sahun manyan abokan Nura M Inuwa. Wanda duk cikin abokan Nura ba wanda yake watsi da baragaza da naira kamar Adam A Zango.

Dandalin Kannywood: Shahararren mawaki Nura M. Inuwa zai angwance
Dandalin Kannywood: Shahararren mawaki Nura M. Inuwa zai angwance

KU KARANTA: Zamu shigo da sabbin jiragen kasa 20 - Ameachi

Abin burgewa da sha'awa shine, Ali Nuhu da shi ake ta gudanar da shagalin bikin auren Nura M Inuwa. wanda abaya wasu sunata zargin ba'a ga maciji tsakanin su.

Acikin mata kuwa Nafisa Abdullahi da Fati Washa sune amara kirjin biki. Waka da yawa sun yi wakokin auren Nura M Inuwa amma Umar M Shareef shine ja gaban su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma wasu mawakan ne ke bayani

Asali: Legit.ng

Online view pixel