Mugun nufi: Yadda aka nemi a kashe shugaba Buhari
Jaridar Desert Herald tayi wani bincike inda ta gano yadda rashin lafiyar shugaba Buhari ta kaya da kuma yadda aka nemi a sa masa guba. Sai dai ba za a iya cewa rahoton ya cika gaskiya dari-bisa-dari ba
Jaridar Desert Herald a wani dogon rahoto da ta fitar ta bayyana cewa an yi yunkurin kashe shugaba Buhari ne kwanaki har ta kai aka zura da shi Asibiti a Landan. Hakan ba zai zo da mamaki ba musamman yadda shugaba Buhari yake da makiya cikin barayin kasa da ‘yan shi’a da masu neman kasar Biyafara.
An bayyana cewa akwai sakaci da rashin sanin aikin tsaro a Fadar Villa har musamman mai kula da al’amuran yau da kullum watau Sarki Abba wanda ‘Da ne wurin Marigayi Alhaji A. Salihijo wanda yayi aiki da Buhari a PTF. Cikin dai wadanda ake zargi da sakaci akwai Sojoji da sauran Jami’an tsaro Inji Desert Herald.
KU KARANTA: Abin da ya sa El-Rufa'i ya rubutawa Buhari wasika
Kowa dai ya san shugaba Buhari ba mutum bane mai rashin lafiya sai ga shi wannan karo sai da aka yi ta masa karin jini. Kai bari ma dai Likitoci ba su taba tunanin Muhammadu Buhari zai tashi ba. Kusan abin da aka bayyana masa kenan a lokacin da shugaban Fastocin Angilikan ya kai masa ziyara.
Yanzu haka dai an sa tsohon Dogarin Marigayi shugaban kasa Janar Abacha watau Hamzah Al-Mustafa yayi bincike game da batun. Wadanda ake zargi dai sun hada da ‘yan shi’a da wasu abokan hamayyar shugaba Buhari da ke cikin Villa har ma da wasu manyan Sarakuna.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng