Matukin jirgin sama ya rasu yana tukin jirgi SV 1734 a kasar Saudiyya
Rayuwa da mutuwa a hannun Allah suke. Babu wanda ya san lokacin da zai cika. Idan muka waye gari ko muka kwanta bacci, ko shakka babu munada shirin yi wani abun domin cigaban rayuwa. Duk da cewa mun san wata rana zamu cika ba tareda karashe aikin da muke niyyan yi ba.
A yau zamuyi Magana akan wani direban jirgin kaar saudiyya wanda ya rasu yana tukin jirgin sama. A ranan, 1 ga watan Maris, jirgi mai lamba Flight SV 1734 ta tashi daga filin jirgin saman Bisha zuwa birnin Riyadh. Komai na tafiya daidai kawai sai wani abin mamaki da ban tsoro ya faru.
KU KARANTA: Sojan kasar Amurka ya musulunta bayan mukabala
Direban jirgin mai suna Waleed Al-Mohammed, wanda an tabbatar yanada lafiya da samu ciwon zuciya. Anyi iyakan kokari amma lokaci yayi. Amma da gaggawa suna sararin samaniya, mataimakinsa ya cigaba da tukin jirgin har suka sauka a babban filin jirgin saman King Khaled dake birnin Riyadh.
Allah ya jikanshi da rahma, mu ma idan lokacinmu yayi ya sa mu cika da kyau da imani.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng