Yan fim sun wataya wurin sunan sambaleliyar diyar Adam Zango

Yan fim sun wataya wurin sunan sambaleliyar diyar Adam Zango

- Jiya ne aka yi bukin sunar ‘yar shahararren mawaki kuma jarumi a wasan fina-finan Hausa Adam Zango a garin Kaduna

- Amaryan Adam Zango, Ummul Kulsum ne, ta haifa wa jarumin ‘yar sa ta mace ta farko acikin jerin ‘ya’yansa wanda duk maza ne ranar Talatar da ta gabata

Yan fim sun wataya wurin sunan sambaleliyar diyar Adam Zango
Yan fim sun wataya wurin sunan sambaleliyar diyar Adam Zango

Tun daga wannan rana ne Adam Zango yake ta sanar wa aminansa da abokanan aikinsa domin su taya shi murna akan hakan.

Adam Zango yace bai taba yin bukin suna ba amma zai yi bana saboda Allah ya bashi abun da yake ta nema wato ‘ya mace.

Ya gode wa Allah da irin zumunci da abokanai da masoya suka nuna masa da iyalansa a wannan rana.

Abokanan arziki da masoya ne suka ziyarci bukin sunan Murjanatu.

A wani labarin kuma, Jaruma ‘yar wasan finafinan Hausa Jamila Umar Nagudu ta karyata rade-radin da ake ta yadawa wai Allah yayi mata rasuwa.

Jamila ta ce tana nan cikin koshin lafiya bata mutu ba kuma.

Ta fadi hakanne a wata sako na bidiyo da ta saka a shafinta na Instagram jiya Asabar.

A bidiyon Jamila ta ce a wannan lokacima za ta yi tafiya ne zuwa garin Kaduna daga Kano.

Tare da yan uwanta tana wasa da raha a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel