Lokacin aurena ne bai yi ba inji Jamila Nagudu

Lokacin aurena ne bai yi ba inji Jamila Nagudu

- Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Jamila Nagudu ta shaida wa majiyar mu cewa ba ta da saurayi a cikin masu yin fina-finan.

- Sai dai ta kara da cewa idan ta gamu da wanda ranta ke so a cikin abokan aikinta ba za ta yi kasa-a-gwiwa wajen aurensa ba.

Lokacin aurena ne bai yi ba inji Jamila Nagudu
Lokacin aurena ne bai yi ba inji Jamila Nagudu

Fitacciyar jarumar ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa 'yan fim cewa ba sa son yin aure, tana mai cewa idan lokacin yin auren mutum bai yi ba babu yadda za a yi ya yi da kansa.

A cewarta, Mutanen da suke cewa ba ma son zaman aure, su dubi sauran al'umma mana. Akwai mata da yawa wadanda suka girme ni amma ba su da aure saboda Allah bai sa lokacin yinsu ya yi ba.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Kano ya aurar ya kuma yi jika a rana guda

Ita kuma Shahararriyar 'yar fim din Kannywood din nan, Hadiza Gabon, ta ce tana so ta yi aure amma lokaci ne kawai bai yi ba.

Da take hira da majiyar mu, Hadiza ta ce aure lokaci ne, kuma kamar mutuwa, idan Allah ya kawo shi babu yadda mutum zai guje masa.

Jarumar, wacce ta lashe kyautar 'yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim ta Africa Films Awards na bana, ta ce tana kaunar duk masu goyon bayanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel