Shugabannin Jam’iyya Suna Ta Sulale wa Suna Barin Peter Obi da Kwankwaso a NDC
- Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar NDC, Abdulmumin Abdulsalami, ya yi murabus ana cikin yin kamfe
- Ya ce ana yi masa rashin adalci kuma wasu manyan jami’an jam’iyyar ne ke hana shi yin ayyukansa yadda ya kamata
- Abdulmumin Abdulsalami zai koma harkokinsa maimakon ci gaba da zama a jam’iyyar da yake ganin ba ta san darajar shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na NDC, Mista Abdulmumin Abdulsalami, ya yi murabus daga jam’iyyar hamayyar.
Abdulmumin Abdulsalami ya bar jam’iyyar, yana mai zargin ana yi masa rashin adalci, ana ware shi sannan manya suna yi masa katsalandan.

Source: Twitter
Mataimakin kakakin NDC ya rubuta takardar murabus
Abdulsalami ya sanar da wannan a cikin wasiƙar murabus da ya aika wa Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Moses Cleopas a cewar Punch.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027
Tsohon mataimakin kakakin NDC ya aika takardar ta hannun shugaban jam’iyyar na mazabarsa ta Nagazi a Ƙaramar Hukumar Adavi da ke Jihar Kogi.
An yi wa wasiƙar mai take ne da ‘Murabus Daga Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress: Janyewa Daga Dukkan Ayyukan Siyasa Na Jam’iyyar’
Meyasa sakataren yada labaran NDC ya bar jam'iyya?
A nan ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan ya fahimci gudunmawar da yake bayarwa ta ci karo da muradun wasu manyan mutane a NDC.
Ya kuma bayyana cewa yawan korafe-korafen da yake yi kan rashin adalci ne suka sa ya yanke shawarar kare lafiyarsa da kwanciyar hankalinsa.
Abdulmumin Abdulsalami ya rubuta:
“Kasancewata ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar NDC, tare da kasancewata jagora mai muhimmanci a lokacin da ake gina jam’iyyar, ya sa na ga ya zama wajibi in fice daga cikinta bisa radin kaina, bayan na fahimci cewa gudunmawar da na bayar cikin gaskiya da kyakkyawar niyya wajen haɓaka jam’iyyar da samun nasararta cikin ɗan lokaci ta ci karo da muradun wasu tsirarun manyan jami’ai masu ƙarfin iko waɗanda ke tafiyar da harkokin jam’iyyar.
“Bugu da ƙari, wannan mataki mai wahala shi ne mafi alheri a gare ni, domin na fi son kwanciyar hankalina maimakon ci gaba da yin korafe-korafe kan jerin rashin adalcin da ake yi mani.”
Matsayin da ya rike a jam'iyyar NDC
Abdulsalami ya taɓa zama shugaban riƙo na jam’iyyar NDC a Jihar Kogi, kafin daga bisani ya zama Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa.
Vanguard ta ce ya kasance Mataimakin Darakta na Ƙasa mai kula da ƙungiyoyin ƙwadago da na farar hula.
‘Da siyasar ya gode wa Jagoran Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Henry Dickson, bisa damar da ya ba shi, tare da nuna godiya ga abokan aikinsa a NWC.
Har ila yau, an ce ya gode wa ƙungiyoyin farar hula da kuma ’yan jarida da suka yi aiki tare da shi a lokacin da yake shugabanci a jam'iyyar adawar.

Kara karanta wannan
Yadda ‘yan sanda suka garkame Farfesa Zulum saboda ya nemi tsayawa takara a Borno
Akwai matsala ne a cikin jam'iyyar NDC?
Da aka tambaye shi mataki na gaba, Abdulsalami ya shaida cewa zai cigaba da harkokin gabansa maimakon irin wannan zaman siyasa mara dadi.
Wasu suna ganin akwai matsala a jam'iyyar NDC ganin yadda shugabanni da wadanda aka ba damar tsayawa takara suke tafiya ko canza sheka.
Sai dai Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na NDC, Osa Director, ya yi watsi da zargin cewa ana fama da wani rikicin gida a cikin jam’iyyar hamayyar.
An ji shi yana mai cewa ficewar mutum guda ba ta isa a ce jam’iyya sukutum tana fuskantar matsala ba.

Source: Twitter
Na hannun daman Peter Obi ya koma SDP
A makon nan ne kuma aka samu labari Peter Obi ya rasa mutumin da bai da irinsa a Arewa, Yunusa Tanko ya koma goyon ‘dan takaran SDP.
Yunusa Tanko ya shiga sahun dakarun Obidient da suka yi watsi da Obi da takarar shi a NDC, yanzu yana tallar SDP a takarar shugaban kasa.
Kafin yanzu ya kasance shugaban 'yan Obidient a duk Najeriya kuma har mulkin Najeriya ya nema a 2019, amma bai kai labari ba a lokacin.
Asali: Legit.ng

