Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016

A farkon wannan mako ne muka kawo jadawalin gwarazan jaruman Kannywood na wannan shekara ta 2016. Wannan karon mun koma bangaren mata domin nuna irin tasu bajintar a bangaren Fina-finan Hausa.

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016

Kamar yadda kuka sani mata na taka rawar gani sosai a harkan fina-finan Hausa, kuma suna daga cikin wadanda ke bunkasa shirin fina-finai na Hausa.

1. Hadiza Aliyu (Gabon)

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Hadiza Aliyu Gabon

Jaruma Hadiza Aliyu kamar yadda ake mata lakabi da Gabon kasancewar ta fito daga kasar Gabon, ta kasance shahararriyar jaruma a matakin farko. Babu tantama wannan jaruma ta nuna kanta a cikin shirin fim din BASAJA GIDAN YARI CIKIN KWARAEWA.

Babu wani abu da za a iya cewa game da ita sai sambarka. Hakika babbar nasara ce a wajen jarumar da ta zamo cikin jerin wadanda suka taka rawa a cikin fim din Basaja. Ta shiga tarihin da ba za a manta da ita ba, domin kusan kowa ya fi ganin ta fiye da sauran jaruman.

Jarumar ta shigo masana’antar finafinai da kafar dama, domin kuwa ta samu nasarar bankwarawa tare hawa bigiren da dukkan wani shahararre yake buri.

Fitacciyar jarumar ta lashe kyautar ‘yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim, a wani bikin bayar da kyaututuka ta Africa Films Awards na shekarar 2016 wanda jaridar Africa Boice take gudanarwa a kasar Ingila.

2. Hafsat Idris

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Hafsat Idris

Jaruma Hafsat Idris ta kasance sabuwa a harkar shirya fina-finai, kuma fim din da ta fara haskawa a ciki shine BARAUNIYA, duk da kasancewar shi fim dinta na farko, jarumar ta samu karbuwa sosai da samun yabo daga masana harkokin finafinan.

Cikin shekara daya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo tauraruwar da kowane lungu da sakon ake labarinta. Gwana ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka kowace irin rawa da aka dora ta.

Da farko an yi tsammanin Hafsat Idris za ta rika fitowa ne a matar aure kawai, amma daga bisani sai kwarewarta ta fito fili ta yadda take iya fitowa a finafinai kala-kala.

Babban abin da ya fi jan hankalin makallata finafinan Hausa game da jarumar shi ne, irin salon kifta idonta a lokacin da take magana. Wasu na ganin jarumar ta fito da nata irin salon ne domin ta kwashi magoya baya, wanda yanzu haka take samunsu a kullu yaumin.

Finafinan da suka sanya jarumar ta haye sahu na biyu a wannan jadawali sun hada da; Furuci, Dan Kurma, Maya, ‘Yar Fim, Wazeer da sauran su.

3. Rahma Sadau

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Rahma Sadau

Duk da badakalar korar jarumar a karshen shekarar nan da ta kunno kai, hakan bai hana Rahma samun kanta a jerin jarumai mata da suka haska a 2016 ba, domin za a iya cewa jarumar ta samu nasarar tsallake Arewacin kasar zuwa Kudancin Nijeriya, Afrika da ma kasashen duniya.

Ta wata fuskar, za a iya cewa korar Rahma daga masana’antar Kannywood gobar titi ce a Jos, domin yanzu ba jarumar Hausa ba ce, tuni ta fara mafarkin fitowa a finafinan industirin da babu kamarta watau Hollywood kungiyar shirya finafinai na kasar Amurka.

Hakika shekarar 2016 ta zowa jarumar da abu biyu; farko kalubalen kora daga abokan aikinta na asali watau Kannywood, da kuma nasarar samun gayyata zuwa Hollywood. Yanzu haka akwai fim dinta na Turanci mai suna SONS OF THE CALIPHATE da ake haskawa a gidan talabijin na Ebony Libe.

4. Nafisa Abdullahi

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Nafisa Abdullahi

Nafisa jaruma ce da ta kware wajen iya salon aktin na soyayya ko kuma salihanci. Tana yin kyau kwarai idan ta fito a matsayin wadda ake zalunta. A shekarar nan ta fito a shirin fim mai dogon zango wanda Darakta Malam Aminu Saira ya bada umarni, watau LABARINA. Tallar shirin kawai aka gani, amma tuni mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu game da rawar da Nafisa ta taka.

Game da gidauniyar da ta bude kuwa, Nafisa ta ce dalilin da ya sa ta kaddamar da wannan Gidauniya ta kuma fara da taimakon talakawa shi ne, bisa rahoto da ta samu na irin matsaloli da al’umma ke fuskanta musamman na rashin dan abin da za a kai bakin salati. A cewarta, lokaci ya yi da ya kamata mutane irinsu su fara taimakawa jama’a ta hanyoyin da suke ganin za su iya.

5. Jamila Umar (Nagudu)

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Jamila Umar Nagudu

Gwana ta gwanaye, wadda aka hakikance tana hawa kowane irin rol, kuma ta aiwatar da shi yadda yake a rubuce, ko ma fiye da haka. An ga haka finafinai sama da 100 da jarumar ta fito ciki a tsawon shekarun da ta yi a Kannywood.

Nagudu ta kware sosai a fagen nishandatar da mutane, musamman a finafinai masu ma’ana da suke dauke da sako. Babu shakka jarumar tana ci gaba da rike kambinta na jarumar da masana’antar ke alfahari da ita.

A shekarar 2016, jarumar ta haska sosai finafinai masu matukar kyau, kadan daga akwai INDON BIRNI, wanda ci gaba ne na Indon Kauye, shiri ne ba barkwanci da ya nishadantar da ‘yan kallo matuka.

Har ila yau fim din Zinaru, wanda shi ma jarumar ta fito a matsayin kwadayayyiyar kaza, Jamila ta taka rawa kwarai da gaske, domin ‘yan kallo sun kara tabbatar da cewa Nagudu ba daga nan ba wajen aktin.

6. Fatima Abdullahi (Washa)

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Fatima Abdullahi (Washa)

Washa ta kasance jaruma mai tashe, wadda cikin kankanin lokaci ta shiga sahun manyan jaruman da ake labarinsu game da kwerawa da suke da ita a wajen amfani da kwalkwalwa a farfajiyar shirya finafinai.

An ga yadda jarumar ta baje kolin basirarsa a fim din BASAJA GIDAN YARI. Darakta Falalu ya nuna cewar shi kwararre ne da ya iya jan zarensa a fannin bada umarni. Ya wahalar da mutane matuka kafin ya bayyana wace ce asalin Washa a labarin. A bangaren Fati kuwa, kusan gaba daya za a iya cewa fim din nata ne, domin tana bayyana kwata-kwata hankulan mutane ya karkata zuwa gare ta.

Da ma Fati Washa ba daga nan ba, sai kuma ga shi ta shiga tsakiyar tsararrakinta, inda ta baje kolin tata basirar, ta kuma samu shiga wannan jerin na matan da suka fi haskawa a shekarar 2016.

7. Maryam Gidado

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Maryam Gidado

TALAKA BAWAN ALLAH, fim ne da Babban Darakta Sunusi Oscar 442 ya bada umarni. Labarinsa ya nuna yadda wani attajiri ke wadaka da dukiya shi da ‘ya’yansa, ba tare da ya san cewar dukiyar ba tasa ba ce.

Gidado da ta saba fitowa a matsayin jarumar da take shan wahala a hannun mugaye, wannan karo ta fito a rol din da ita ce ta uzzarawa wata saboda wanda take so yana nuna ba ya son ta, waccan yake so.

An ga yadda take nuna salon fitsara da rashin kunya, zobaro baki da yin daurin dankwalin ture ka ga tsiya. Har ila yau, akwai tallan wani fim mai suna Nana Habiba, wanda shi ma a ciki jarumar ta yi bajinta sosai, musamman da yake ta fito a matsayin wadda aka sace ake kuma kokairn yanka ta.

Babu shakka wannan jarumar har yanzu tana jan zarenta yadda ya kamata, sam ta ki yarda ya tsinke.

8. Aisha Aliyu (Tsamiya)

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Aisha Aliyu Tsamiya

Duk da cewar jarumar ba kowane rol take karba ba, tana tsayawa ta zaba tare darjewa, ta yi finafinai masu ma’ana wadanda suka birge ‘yan kallo.

Wasu finafinan ta fito ita kadai, yayin da wasu kuma suka fito da yawa. Misali MIJIN BIZA na kamfanin Abnur, wanda Abdul Amart mai kwashewa ya shirya, Falalu A. Dorayi ya bada umarni akwai ‘yan wasa da yawa. Duk da ta fito a tsakiyar jarumai mata da yawa, hakan bai hana ta daga yatsa tare da nuna tata bajintar ba.

Har ila yau fim din ‘Yar Amana wanda suka fito tare da jarumi Adam A. Zango da Isah Adam (Feroz Khan), an ga yadda a cikin wannan shiri jarumar ta kara bayyana kanta a matsayin kwararriyar da duniyar finafinai ke alfahari da ita

9. Sadiya Adam

Kannywood: Taurarin jarumai Mata 10 da suka fi haskawa a 2016
Sadiya Adam

Farin jinin da ta samu cikin kankanin lokaci ya yi matukar bawa masu kallon finafinan Hausa mamaki. Jarumar haifaffiyar garin Maiduguri a jihar Borno, ta shigo masana’antar fim da kafar dama, domin sunanta ya fara amo a bakuna makallata finafinan Hausa.

Shekarar 2016 abin alfahari ce ga Sadiya Adam, domin ta fito a cikin finafinan masu kyau, wadanda suka zamo mata wani mataki na darewa duniyar shahara, tuni ta fara samun tallace-tallace daga kamfononi a nan gida Nijeriya.

Finafinan da fito a wannan shekara sun hada da; Bani Ba Aure, Hali Daya, Auren Manufa, Hasashe, Gwarzon Shekara da Wutar Gaba.

10. Hannatu Bashir

Mutane da yawa sun yi mamakin ganin yadda jarumar ta lashe kyautar gwarzuwar mai taimakawa jarumar a gasar da Mujallar City People ke gabatarwa duk shekara a Legas.

Hannu ta lashe wannan kambi na 2016 sakamakon irin rawar da ta taka a finafinan Hausa masu kyan gaske.

Hakika wannan jaruma ba za ta man da shekarar 2016, domin a cikinta ne ta samu damar tattaki har zuwa birnin Ikko ta karbo kambi da kowace jaruma ke mafarkin samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng