Zidane zai kafa tarihin da yan Bacelona ba za su so ba (Karanta)
Real Madrid ta kara bajintar yin wasa 36 ba tare da an doke ta ba, inda ta casa kungiyar Club America 2-0 ta kai wasan karshe na cin kofin duniya na kungiyoyi.
Karim Benzema ne ya fara ci wa Zakarun na Turai, Real Madrid, kwallo a daidai lokacin da za a tafi hutun rabin lokaci a wasan da ake yi a Japan, bayan da Toni Kroos ya tura ma sa kwallo.
Bayan an dawo wasa, ana dab da tashi ne a karin lokaci, sai Cristiano Ronaldo, ya kara ta biyu, amma kuma an samu rudani kan tabbacin shigar kwallon raga.
Daga nan ne sai alkalin wasa Enrique Caceres, ya bukaci bayanin mataimakinsa mai duba hoton bidiyon wasan, inda daga nan ne ya tabbatar da ta ci.
An dai fara amfani da tsarin mataimaki alkalin wasa mai duba hoton bidiyon a wasa a gasar ta bana, domin taimaka wa alkalin wasa warware duk takaddamar da ta taso wadda ba a iya gani ko tantance ta ba a lokacin wasan.
Yanzu Real Madrid za ta fafata a wasan karshe da Zakarun Asia, Kashima Antlers ta Japan, wadda ranar Laraba ta doke Atletico Nacional ta Colombia 3-0, a daya wasan na kusa da karshe.
Idan har kungiyar ta Real Madrid ta lashe gasar to mai horar da ita watau Zidane zai kafa wani muhimmin tari inda zai bi jerin sahun yan wasa kalilan da suka taba lashe kofin a matsayin dan wasa da kuma mai horar wa.
Asali: Legit.ng