Kyawawan halayen Hadiza Gabon

Kyawawan halayen Hadiza Gabon

Hadiza ko kuma Dijatou Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, tana daya daga cikin jarumai mata da suka shahara a farfajiyar finafinan Hausa. Hadiza ta yi matukar kwarewa a duk wani matsayin da za a ba ta a fim, wanda hakan ya sa har yau ake damawa da ita a masana’antar, domin ba kowace jaruma ba ce za ta iya hawa irin matsayin da jarumar ke hawa a finafinai.

Kyawawan halayen Hadiza Gabon
Fitacciyyar Jarumar Kannyywood, Hadiza Gabon

Kyakkyawar jarumar ta kuma kasance mai yawan masoya daga cikin jaruman fim, har ta kai ga ta samu daukakar da ita kanta ba ta taba zaton samu ba.

Allah ya azurta jarumar da kyawawan dabi’u na taimako, tausayi da jin kan mutane, musamman gajiyayyu, marasa karfi da kuma marayu.

Akwai lokacin da labarin wata nakasashiyar yarinya mai suna Rahama Karuna wacce ake dauka a cikin roba ana bara da ita a jihar Kano, lokacin da Hadiza ta ji labarin wannan yarinya sai ta tausaya sosai harma ta ziyarci yarinyar inda ta tallafa mata da kudade da kayayyakin abinci.

KU KARANTA KUMA: Mayan mutane sun halarci auren yarinyar shugaban kasa

Sannan kwanakin baya Hadiza ta ziyarci sansanin yan  gudun hijira inda su ma tayi masu alkhairi mara misali, domin ta tallafa masu da kayan abinci, kamar yadda muka sani cewa yan gudun hijira sunyi fama da lalurar yunwa.

Kyawawan halayen Hadiza Gabon
Hadiza Gabon a lokacin da ta kai ziyara sansanin yan gudun hijira

Bayan nan kuma a lokacin da jaruma Hadiza za ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta, maimakon ta tara jama’ar da ba su dace ba a yi ta sharholiya, sai ta tattara kayayyakin bikin nata ta je gidan marayu, inda ta dauke su a matsayin wadanda za su taya ta bikin.

Hadiza ta yanka kek din bikin ranar haihuwarta ta tare da marayun kuma ta ci ta sha tare da marayun, domin a cewarta yin hakan wata hanya ce ta farantawa marayun rai, tare kuma da debe musu kewa, wanda bai kamata a ce ana mayar da su saniyar ware ba a al’amuran farin ciki dake gudana a kasar nan.

Kyawawan halayen Hadiza Gabon
Hadiza Gabon tare da wasu yara

Wannan ba shi ne karo na farko da Hadiza ta kai ziyara gidan marayu ba, domin aikinta ne ziyara gidan marayun inda take raba musu kayan abinci da kayan sawa.

Munayi wa wannan jaruma fatan alkhairi da kuma ci gaba a rayuwarta ta duniya da lahira.

https://youtu.be/f-N708faAd4

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng