An caccaki Ronaldo saboda cin mutuncin addinin Buddha

An caccaki Ronaldo saboda cin mutuncin addinin Buddha

An soki lamirin shahararren dan wasan kwallon kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo bayan ya daura hotunansa a kafafen sadarwa inda ya daura kafa daya akan gunkin Buddha.

An caccaki Ronaldo saboda cin mutuncin addinin Buddha
Dan wasan kwallon kafa, Ronaldo Christiano

Hoton ya harzuka mabiya addinin Buddha inda suka dinga sukar dan wasan da munanan kalamai, inda har wasu ma suka ce sun janye goyon bayan da suke masa. Sa’annan suka bukaci ya cire hoton.

Tsananin ya sanya wasu daga cikin mabiya addinin suka dinga yi mai mugun fata, inda wasu suka yi mai addu’ar kwallonsa ta lalace.

KU KARANTA: Barawao ya yaba ma aya zaki a hannun jama’a

An caccaki Ronaldo saboda cin mutuncin addinin Buddha

Jama’a da dama suna ganin ubangijin Budha yafi karfin a wulakanta shi, saboda suna tunanin nasarar da kungiyar Leicester ta samu na lashe gasar Firimiya na bara yana da nasaba da goyon bayan da wasu shehunnan malaman addinin Buddha suka baiwa kungiyar.

Shehunnan malaman sun yi ma kungiyar addu’ar neman sa’a ne a wani gidan bautansu dake cike da gumakan addininin Buddha, inda mataimakin shugaban gidan Abbott Phra Prommangkalachan ya jagoranci wani addu’ar neman sa’a ga kungiyar.

Zaku iya duba wasannin da za’a buga a gasar Firimiya na kasar ingila tare da sakamakon wasannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng