Rikcin APC: Akinfewa yace maganin Bola Tinubu kenan

Rikcin APC: Akinfewa yace maganin Bola Tinubu kenan

Sanata Mojisoluwa Akinfewa yace Allah ne ya kama Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC

Sanata Akinfewa yace kowa ta shi ta fice shi a siyasar.

Matasan APC sun kira Cif Oyegun ya sauka daga kujerar sa na Shugaban Jam’iyyar ta Kasa

Rikcin APC: Akinfewa yace maganin Bola Tinubu kenan
Asiwaju Tinubu

 

 

 

 

Sanata Akinfewa na Jam’iyyar AD yace babu wanda ya kamata ya ji tausayin abin da ke faruwa da Bola Tinubu. Da alamun cewa an dai maida Bola Tinubu saniyar ware a cikin Jam’iyyar ta su ta APC, sai dai Akinfewa yace Allah ya ƙara.

Sanata Mojisoluwa Akinfewa, wanda shine Shugaban Majalisar BOT ta dattawa na Jam’iyyar AD, yace Allah ne ya kama Tinubu. Akinfewa ya bayyana hakane ga manema labarai a Jiya, Talata. Jaridar Punch ta rahoto cewa Sanata Akinfewa yace ba zai goyi bayan Tinubu ba kamar yadda sauran Yarbawa ke yi. Sanata Akinfewa wanda ya rike Shugaban Jam’iyyar AD yace rabon sa da magana da Bola Tinubu, yau fiye da shekaru 15.

KU KARANTA: Bukola Saraki da Ekweremadu na cikin matasala

Sanata Mojisoluwa Akinfewa yace Bola Tinubu ya jefa kan sa cikin matsala ba wani ba, don haka kar ma a kira sunan sa a cikin wannan rikici. Sanata Akinfewa yace Bola Tinubu bai isa ya sa ya fara goyon bayan sa ba, yace yayi kadan.

Wata Kungiyar matasa ta APC mai suna PYL tace Cif Oyegun karyayyaki kurum ya sheka a martanin da ya rubuta ga Bola Tinubu, ta kuma nemi ya sauka daga matsayin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: