Mario Zagallo: An Yi Rashi a Duniyar Kwallon Kafa Bayan Tsohon Dan Wasan da Ake Ji da Shi Ya Rasu

Mario Zagallo: An Yi Rashi a Duniyar Kwallon Kafa Bayan Tsohon Dan Wasan da Ake Ji da Shi Ya Rasu

  • Duniyar ƙwallon ƙafa ta yi babban rashi na shahararren ɗan wasa kuma koci Mario Zagallo wanda ya rasu a ranar Juma'a
  • Mario Zagallo na ƙasar Brazil shi ne mutum na farko da ya taɓa lashe gasar cin kofin duniya yana a matsayin ɗan wasa da koci
  • Zagallo wanda suka taka leda tare da Pele ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 92 a duniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Brazil - Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Brazil kuma mutum na farko da ya taba lashe gasar cin kofin duniya a matsayin ɗan wasa kuma koci, Mario Zagallo, ya rasu yana da shekara 92 a duniya.

Zagallo ya kasance mai taka rawar gani kamar kowa a cikin ɗaukakar Brazil a matsayin mai ƙarfin ƙwallon ƙafa a duniya, cewar rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga har fada sun yi awon gaba da babban basarake

Mario Zagallo ya kwanta dama
Mario Zagallo ya yi bankwana da duniya Hoto: eurosport.com
Asali: UGC

Ƴaushe Zagallo ya rasu?

Zagallo, wanda ya mutu a ranar Juma'a, shi ne ɗan wasan Brazil ɗaya tilo da ya rage daga cikin tawagar da ta lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 1958, wanda shi ne na farko da ƙasar ta lashe, rahoton Livescore ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarar ƙasar na cin gasar cin kofin duniya a shekarar 1958 ta zo ne bayan ta yi rashin nasara shekara takwas kafin nan a hannun ƙasar Uruguay.

A lokacin Zagallo ya bayyana cewa:

"Na kasance a Maracana a wannan rashin nasarar da muka yi a hannun Uruguay. Ni soja ne kuma aikina ne in hana mutane shiga filin wasa.
"Ba zan taɓa mantawa da shirun da aka yi da baƙin ciki da kuma takaicin wannan cin kashin ba."

Shahararren abokin wasansa, Pele, ya mutu a watan Disamban shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Rusau: Yan kasuwan Kano sun shigar da korafi wurin yan sanda kan Gwamna Abba da Kwankwaso

Zagallo ya taka rawar gani sosai a Brazil

Zagallo ya taimakawa ƙasar Brazil wajen lashe gasar kofin duniya har sau huɗu a lokacin da yake taka leda.

Bayan ya yi ritaya, Zagallo ya dawo wasa a matsayin manaja, inda ya karɓi tsohon kulob ɗinsa na Botafogo, ya kuma kai su ga lashe kofunan jiha sau biyu a lokacin da ƙasar take ƙarƙashin mulkin kama-karya na soja.

Matarsa ​​wacce suka kwashe shekaru 57, Alcina de Castro, ta rasu a shekarar 2012.

Ɗan Wasan Najeriya Ya Rasu a Fili

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan wasan Najeriya mai suna, Sodiq Adebisi, ya riga mu gidan gaskiya yayin da je ɗaukar horo tare da sauran ƴan wasa a jihar Ogun.

Ɗan wasan ya rasu ne jim kaɗan bayan ya yanke jiki ya faɗi a filin wasan 'Dipo Dina International Stadium' da ke garin Ijebu-Ode.

Asali: Legit.ng

Online view pixel