Tsohon Dan Wasan Ƙwallon Ingila Trevor Francis Ya Rasu Yana Da Shekaru 69 a Duniya

Tsohon Dan Wasan Ƙwallon Ingila Trevor Francis Ya Rasu Yana Da Shekaru 69 a Duniya

  • Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Ingila, Trevor Francis ya rasu yana da shekaru 69
  • Makusantansa sun bayyana cewa Francis ya rasu ne a ƙasar Spain sakamakon bugun zuciya
  • Francis ya kasance ɗan wasan ƙwallon ƙafar Burtaniya na farko da aka fara saya a kan fama miliyan ɗaya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon dan wasan Ingila Trevor Francis ya mutu yana da shekaru 69 sakamakon bugun zuciya da ya gamu da shi a Spain.

A 1979, Trevor ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Burtaniya na farko da aka saya akan fam miliyan 1, inda ya tashi daga Birmingham City zuwa Nottingham Forest.

Dan wasan Ingila Trevor Francis ya kwanta dama
Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Ingila Trevor Francis ya rasu yana da shekaru 69. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Wasu daga cikin nasarorin da ya samu a lokacin da yake taka leda

Ya lashe gasar cin kofin Turai guda biyu a lokacin da yake Forest a shekarar 1979, da kuma 1980 inda ya yi nasara a kan Malmo kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matasa Na Kona Hoton Mawaki Davido a Maiduguri Ya Bayyana, Sun Nemi Ya Yi Abu 1 Rak

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Francis ya kuma ci wa Ingila wasanni 52, inda ya ci ƙwallaye 12 kafin ya fara aikin horar da ‘yan wasanni.

Bayan da Forest ta lashe gasar cin kofin Turai sau biyu, Francis ya koma Manchester City kafin yin wasa tare da ƙungiyoyin wasanni na Italiya Sampdoria da Atalanta.

Ya shafe zangon wasa ɗaya a Scotland tare da 'yan Rangers, kafin daga bisani ya koma Queens Park Rangers, inda a nan ma ya zama manajan-yan wasa.

Ya yi ritaya a matsayin dan wasa a hukumance a 1994, jim kadan kafin cikarsa shekaru 40, wanda ya zuwa lokacin ya buga wasanni 632, inda ya zura kwallaye 235 a raga.

Mutane sun yi jimamin mutuwar Trevor

Sky Sports ta tattaro alhinin rasuwar tasa da wasu daga cikin abokan marigayin suka wallafa a shafukansu na sada zumunta kamar haka:

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Litar Man Fetur Za Ta Dawo Naira 50 Kacal a Najeriya, Fitaccen Malami Ya Faɗi Gaskiya

Tsohon mai tsaron gida na 'yan ƙwallon Ingila ya rubuta:

“Na yi matukar baƙin ciki da jin labarin rasuwar tsohon abokin aikina Trevor Francis mutumin kirki, an yi mummunan rashi.”

Wani ma daga cikin abokansa na ƙwallo Viv Anderson ya ce:

“Yanzu nake jin labarin mara daɗi dangane da Trevor Francis, ya kasance mutum ne mai ban sha'awa kuma ƙwararre, za a yi kewarsa sosai, ina miƙa gaisuwa ga 'yan uwa da abokan arziƙi.”

Kungiyar Al-Hilal ta ƙasar Saudiyya na zawarcin Mbappe kan €300m

Legit.ng a baya ta kawo muku cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya Al-Hilal, ta shirya sayan ɗan wasan PSG, Kylian Mbappe a kan yuro miliyan 300.

Mbappe ya samu matsala ne da ƙungiyar da yake bugawa wasanni wato PSG, kan ƙin amincewa da tsawaita kwantiraginsa wanda zai ƙare a 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel