Cikakken Bayani: Kyautukan Makuden Kudin da Ake ba Kasashen da Suka je Gasar Kwallon Kafa ta Kofin Duniya
- Gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta zo karshe a yau Lahadi inda za a kara tsakanin kasashen Argentina da Faransa a birnin Doha dake kasar Qatar
- Jimillar kudin da za a fitar na kyautuka ga kasashen da suka nuna kwazo har suka halarci gasar ya kai $440 miliyan
- Kasashen da suka fara samun kyauta daga cikin kudin sun hada da wadanda aka fitar tun daga matakin farko har zuwa wacce a yau zata yi nasarar lashe gasar tare da daukar kofin
Makuden kudin da za a bada kyauta na kungiyoyin da suka kasance zakaru a gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da ake yi a Qatar a 2022 ta kai $440 miliyan.
Gasar da ake yi a 2022 ta samu kungiyoyi 32 daga kasashe daban-daban na duniya.
Kamar almara: Wani ya hango nasarar Morocco kan Portugal, 'yan Najeriya sun yi caca a kai, sun ci miliyoyi
13 daga cikin kasashen daga Turai, biyar daga Afrika, hudu daga Amurka ta Arewa, hudu daga Amurka ta Kudu sai shida daga Asia.
Kungiyoyin da suka fice daga gasar tun a matakin farko sun hada da Qatar, Ecuador, Wales, Iran, Mexico, Saudi Arabia, Denmark, Tunisia, Canada, Belgium, Germany, Costa Rica, Serbia, Cameroon, Ghana, Uruguay kuma kowannensu zasu samu $9 miliyan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyoyin da suka je zagayen kasashe 16 sun hada da USA, Senegal, Australia, Poland, Spain, Japan, Switzerland, Korea ta Kudu kuma dukkansu zasu samu $13 miliyan.
Wadanda suka kai ga kwata final sun hada da Brazil, Netherlands, Portugal da Ingila kuma zasu samu $17 miliyan kowannensu.
Kasar da ta kasance ta hudu ita ce Morocco, zata samu $25 miliyan.
Wacce ta dauka na uku ita ce Croata ta zamu $27 miliyan.
Kasar da ta kasance ta biyu tsakanin Argentina ko Faransa za ta tafi gida da $30 miliyan yayin da wanda yayi nasarar lashe gasar zai samu $42 miliyan.
Wannan yawan kudin ya karu daga $40 miliyan na gasar 2018.
Kafin 2016, kungiyoyin da suka yi nasarar lashe gasar kwallon kafa ta duniya bata samun $10 miliyan.
A 2002, an dinga matsantawa FIFA da ta kara yawan kudin kyautar gasar.
Gasar zata zo karshe a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamban 2022.
Najeriya bata smau halarta ba
Tun farko dai kasar Najeriya bata samu halarta ba saboda lallasa ta da aka yi tun a lokacin fitar da kasashen da zasu halarci Gasar.
Asali: Legit.ng