Jihar Zamfara
Tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya koka kan tabarbarewar tsaro inda ya ce matsalar tsaro za ta ragu sosai a yankin Arewa maso Yamma a 2025.
Kakakin rundunar sojoji ya tabbatar da cewa dakarun sojojin 'Operation Fansar Yamma' sun kama wata mata mai shekaru 25 kan zargin tana safarar bindigogi ga ƴan fashi
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya mika ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar gwamnan Jigawa, Hajiya Maryam da babban dansa, AbdulWahab Umar Namadi.
Bello Turji ya sake yin sabon bidiyo inda ya soki hukumomin Najeriya da sojoji kan yada cewa an kama wasu daga cikin yan uwansa da suka mataimakansa ne.
Dakarun Najeriya sun kashe shugabannin 'yan ta’adda Alhaji Ma’oli da Kachalla Muchelli a wani farmaki a Katsina da Zamfara, tare da kawo zaman lafiya ga yankunan.
Kasurgumin dan ta'adda da ya addabi Arewa, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo inda yake gargadi ga hukumomi su sake musu yan uwa ko a fuskanci hare-hare a 2025.
Jami’an tsaro da ‘yan banga sun kashe “Al’jan,” dan ta’adda da ya addabi Tsafe, tare da kawo zaman lafiya ga mazauna yankin da ke fama da hare-hare.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi martani kan dawo da hakar ma'adanai a jihar Zamfara. Ministan ya nuna cewa hakan zai bunkasa tattalin arziki.
Bello Turji ya kafa sabuwar mafaka a dajin Indaduwa, yana kai farmaki, yin garkuwa, da neman karya karfin kungiyar Maniya da tsaron gwamnati a Gundumi.
Jihar Zamfara
Samu kari