Amurka
Shugaba Donald Trump ya karyata jita-jitar mutuwarsa da ta bazu a shafukan sada zumunta, ya ce bai taba jin wannan labarin ba sai da aka tambaye shi.
Shugaban Amurka ya kara taso da maganar korar Falasdinawa daga Gaza domin a kaisu wasu kasashe a kama musu haya a ba su kudin abinci na shekara daya.
Wani luguden wuta na bam daga sojojin Isra’ila ya kashe Firaministan Houthi mai ikirari, Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi, da wasu jami’an ƙungiyar Houthi a Sanaa.
Wani dan Najeriya Daniel Chima Inweregbu ya amsa laifin da gwamnatin Amurka ke tuhumarsa da aikatawa na damfarar soyayya ta intanet, za a hukunta shi.
Yayin da ake shirin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) a watan Satumbar 2025, kasar Amurka ta hana shugabannin Falasɗinu shiga taron a New York.
Rahotanni daga kasar Mexico sun nuna cewabsanatoci su ba hammata iska a zaman ranar Laraba, inda lamarin ya kai ga doke doke da ture-ture a zauren Majalisa.
Shugaban kungiyar 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu ya rubuta wasika ga kasashen duniya kamar Amurka, Isra'ila, Faransa domin su shiga shari'arsa da gwamnati.
Kotun Amurka dai ta daure Sarkin Gargajiya daga jihar Osun na tsawon shekaru hudu da yan watanni bayan kama shi da laifin cinye tallafin cutar COVID-19.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na iya tsige mai martaba Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede bayan kotun Amurka ta daure shi na tsawon shekaru.
Amurka
Samu kari