Amurka
Mahukunta a kasar Iran sun sanar da cafke daruruwan mutane da dama bisa zargin hada baki da Amurka da Isra'ila. Ta bayyana cewa za ta ci gaba da cafke maci amana.
Gwamnatin China ta hannun ma'akkatar harkokin waje ta jadadda kudirinta na shiga tsakani domin kawo karshen fadan da ya barke tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran.
Kafin a kashe shi, Ali Larijani ya gargaɗi Donald Trump cewa kisan shugabannin Iran zai sa al'ummar ƙasar su ƙara zage damtse wajen yakar makiyansu.
Kasashen Musulmi za su yi taron gaggawa a kasar Saudiyya bayan yakin Iran da Amurka/Isra'ila ya ki tsaya a mako na uku. Za su yi taro a birnin Riyadh ranar Laraba.
Shugaban kasar Cuba, Miguel Díaz-Canel ya ce yana daidai da Trump idan ya shiga ksar shi zai kai farmaki. Trump ya nuna cewa zai kwace ikon kasar Cuba.
Rahotanni sun bayyana cewa Rasha na taimakawa Iran da bayanan tauraron dan Adam da fasahar jiragen yaki, ciki har da wuraren sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Ƙungiyar Saraya Awliya al-Dam ta kai hare-hare 50 kan sansanonin Amurka, yayin da Iran da Amurka ke sa-in-sa kan yadda aka kakkabo jirgin KC-135.
A labarin nan, za a ji cewa dubun wani dan leken asiri da keyi wa Isra'ila aiki a Iran ya shiga hannun mahukunta, an aika shi barzahu ana tsaka da yaƙi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya ya yi Allah wadai da harin da Amurka da Isra'ila suka kai Iran a wata sanarwa da ya fitar kan duba watan sallah.
Amurka
Samu kari