Amurka
Kasar Iran ta gargadi Amurka kan tura karin sojoji Gabas ta Tsakiya, tana cewa tana sa ido sosai kan dukkan motsin rundunar yayin da ake ci gaba da yaki.
Fafaroma Leo ya yi kira ga shugabannin kowane banngare da ke yaki a Gabas ta Tsakiya su tsagaita wuta. Ya yi magana ne bayan shiga mako na 3 da yakin Iran da Amurka.
Kungiyar Hezbollah da ke marawa Iran baya ta kai farmaki kan jirgin Isra'ila yayin da ya yi yunkurin kai farmaki a kasar Lebanon. Isra'ila bata ce komai ba.
Gobara ta tashi a wani tsohon ginin da ke dauke da kotu da wasu ofisoshi n gwamnati a Amurka. Hukumomi sun sanar da cewa an dage zaman kotu zuwa wani lokaci.
Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), ta kaddamar da sababbin hare-hare kan Isra'ila. IRGC ta bayyana wuraren da ta farmaka.
Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na tattaunawa da Iran kan wani tsari mai maki 15 domin kawo karshen yaki da kuma batun makamin nukiliya.
Kasashen Pakistan, Egypt da Turkey sun bayyana cewa za su jagoranci zaman sulhu tsakanin Iran da Amurka domin kawo karshen yakin da ake a Gabas ta Tsakiya.
Iran na ci gaba da harba makamai masu linzami kan Isra'ila yayin da ake ci gaba da fafatawa a Gabas ta Tsakiya. Makaman na Iran sun yi barna a wasu birane.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya sanar da cewa Koriya ta Arewa za ta cigaba da mallakar nukiliya. Ya zargi Amurka da keta doka kan kai hari Iran.
Amurka
Samu kari