Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gargadi China cewa za ta fuskanci manyan matsaloli idan ta aika makamai zuwa Iran a yayin rikicin da ake yi a yankin.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce rundunar ruwa za ta kulle mashigar Hormuz tare da dakile jiragen da suka biya Iran kudin wucewa bayan tattaunawa ta gaza.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasarsa a shirye take ta shiga tsakani domin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya yayin da rikici ke ƙaruwa.
Hezbollah ta harba rokoki da jirage marasa matuƙi kan Isra'ila yau Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026, bayan gazawar tattaunawar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka.
Shugaban Majalisar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce duk da niyyar sulhu, ƙasarsa ba ta da cikakken amincewa da ɓangaren da suke tattaunawa da shi.
Kasar Turkiyya ta soki Benjamin Netanyahu kan kalaman da ya yi wa Recep Tayyip Erdogan, tana mai cewa ba shi da halacci ko darajar koyar da kowa.
Kasar Musulunci ta Iran ta zargi Amurka da gindaya sharuddan da suka wuce-gona-da-iri a tattaunawar sulhu da aka gudanar a Islamabad, babban birnin kasar Pakistan.
Amurka da Iran sun kasa cimma yarjejeniya a Pakistan a ranar Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026, bayan sa'o'i 21 na tattaunawa. Ana fargabar yakin na iya barkewa.
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya bayyana cewa sun yi tatttaunawa da Iran da kyakkyawar niyya, kuma sun gabatar da tayi mafi kyau a Pakistan.
Amurka
Samu kari