Amurka
A labarin nan, za a ji cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karbi sunayen mutanen da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tantance don a nada su jakadu.
Jam’iyyar APC ta soki kira da Tanimu Turaki na PDP ya yi na neman kasashen waje su shiga lamurran Najeriya, tana mai cewa hakan rashin kishin ƙasa ne.
Shugaban CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya ce suna maraba da shawarar Amurka ta taimaka wa Najeriya wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da rashin tsaro a ƙasar.
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki ya bukaci shugaban Amurka, Donald Trump da sauran kasashen duniya su kawo dauki dok ceton Najeriya.
Dan majalisar Amurka, Riley Moore ya ce ya san a yankin Kiristoci aka sace daliban GGSSC Maga a jihar Kebbi. Bashir Ahmad ya masa martani kan kuskuren da ya yi.
Majalisar dinkin duniya ta amince da kudirin kafa rundunar tsaron duniya a Gaza. Kudirin zai taimaka wajen kafa kasar Falasdinawa a shekaru masu zuwa.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tiggar ya tabbatar da cewa tattaunawa ta yi nisa da Amurka kan yadda za a hada kai wajen magance matsalolin tsaro.
Majalisar Amurka za ta fara bincike kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya da Donald Trump ya yi. An gayyaci wasu malaman addinin Kirista Amurka kan zargin.
’Yan sanda a New Orleans sun kama wani matashi dan Najeriya, Chukwuebuka Eweni, bisa zargin kashe mahaifinsa da raunata ’yan uwansa mata biyu a cikin gida.
Amurka
Samu kari