Siyasar Amurka
A labarin nan, za a ji cewa harin da Israila ta kai kasar Iran ya jawo asarar rayukan manyan dakarun tsaron kasar, daga ciki har da masu tsattsauran ra'ayi.
Kasar Iran ta sanar da toshe hanyar jirgin ruwa ta Hormuz da ake bi domin jigilar mai a duniya. Toshe tashar jirgin zai iya shafar tattalin arzikin duniya.
Mai kudin duniya, Elon Musk ya fito ya ce ya yi nadama kan wasu kalamai da ya fada a kan shugaban Amurka Donald Trump da suka yi cacar baki a intanet.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya hana 'yan kasashe 12 ciki har da kasashen Musulmi da Afrika shiga Amurka. Trump ya taba sanya dokar a wa'adin farko.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci kasar Amurka yayin wani taron tsofaffin daliban da suka yi karatu da su a Lagos. Ya ziyarci cibiyar sararin samaniya ta NASA.
Tsohon shugaban Amurka Joe Biden, mai shekara 82, na fama da cutar daji mai tsanani da ta bazu zuwa ƙasusuwansa, tuni shugabanni suka fara yi masa fatan samun sauki.
Ɗan majalisar Democrat ya gabatar da ƙudirin tsige Trump, yana mai zargin sa da ayyukan da ba su dace ba. Fadar White House ta kare Trump tare da sukar kudurin.
Bill Gates ya zargi Elon Musk da kashe yaran talakawa a fadin duniya ta hanyar dakatar da ayyukan hukumar USAID. Gates ya ce zai rufe gidauniyarsa a 2045.
Shugaban Amurka ya sanya kayan Fafaroma da aka kirkira a wani hoto. Malaman coci a duniya sun caccaki Trump sai dai fadar White House ta kare Trump kan lamarin.
Siyasar Amurka
Samu kari