Siyasar Amurka
Sakataren tsaron Amurka ya kori sojan Amurka, Laftanar Janar Jeffrey Kruse da ya karyata ikirarin Donald Trump kai cewa ya lalata cibiyoyin nukiliyar Iran a baya.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya laftawa kasashe da dama haraji ciki har da Najeriya. Donald Trump ya kakaba harajin ne bayan wa'adin da ya bayar ya cika.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce suna shirye da su sake kai hari Iran idan hakan ta kama. Ministan harkokin wajen Iran ya ce Amurka ta musu barna.
Trump ya ce harin da Amurka ta kai Tehran ya lalata cibiyoyin nukiliyar Iran, amma rahotanni sun ce wurare biyu za su iya dawowa aiki cikin watanni biyu.
Donald Trump na fama da cutar jini ta CVI da ke hana gudanawar jini da kyau, amma an tabbatar da cewa babu wata barazana ga lafiyarsa kamar yadda likitansa ya fada.
Trump ya gargadi Elon Musk da ce zai iya barin Amurka ya koma Afirka ta Kudu saboda adawarsa ga dokar "Big Beautiful Bill". Musk ya yi barazana ga sanatocin Amurka.
Shugaba Donald Trump ya ce ba zai sake zama a teburin sulhu da kasar Iran ba kan mallakar makamin nukiliya. Ya ce shi ba kamar Barrack Obama ba ne.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce ba su da wata masaniya kan cewa Amurka za ta zauna da su. Donald Trump ne ya ce zai zauna da Iran a mako mai zuwa.
Shugaban Amurka, Donald Trump na shirin shawo kan Iran ta dawo teburin sulhu da dala biliyan 30 da cire mata takunkumi kan mallakar makamin nukiliya.
Siyasar Amurka
Samu kari