Kudu maso gabashin Najeriya
Gwamna Seyi Makinde ya ce PDP tana nan daram da karfinta, kuma ta kara haɗa kan 'ya'yanta a Legas domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da karbo mulki a zaben 2027.
Farashin litar fetur ya ƙaru daga N770.54 a Yulin 2024 zuwa N1,024.99 a Yulin 2025, inda Jigawa, Lagos da Sokoto suka fi tsada, yayin da Zamfara ta fi araha.
NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da tsawa a jihohin Arewa da kudanci ciki har da Abuja, Kano, Kaduna, Oyo, Delta da Lagos a ranar Juma’a, 22 ga Agusta.
Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta ayyana dan takarar LP, Bright Emeke Ngene wanda ke zaman gidan yari a matsayin wanda ya lashe zabe dan majalisa a Enugu.
APC Ogun ta dakatar da Sanata Daniel da Hon. Folarin bisa zargin cin dunduniyar jam’iyya, bayan kin kare kansu da kuma tursasa mambobi su janye ƙorafe-ƙorafe.
An yi ta ce-ce-ku-ce bayan Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya karbi miliyoyin daloli daga bankin raya Musulunci inda daga bisani ya yi karin haske.
Matasan jam'iyyar APC sun fara kokarin jawo ra'ayin gwamnan jihar Enugu domin ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyarsu, sun yi alkawarin mara masa baya a 2027.
NDLEA ta kama dilan kwayoyi Sunday Ibigide a Delta, ta lalata gonakin wiwi a Enugu, ta kuma kwato magungunan buguwa na biliyoyi a Rivers da sauran jihohi.
Rahotanni daga jihar Anambra sun nuna cewa an samu tashin hankali a zaben cike gurbin Sanata Andy Ubah, wanda ya koma ga Allah a watannin da suka shude.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari