Siyasar Najeriya
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kam zaben kananan hukimomin da aka gudanar da jihar. Gwamna Abba ya ce an yi sahihin zabe a jihar.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa shugaban kasa yana da niyya mai kyau ga ƴan Najeriya, ya bukaci a ci gaba da yi masa addu'a.
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sanya dokar taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a faɗin kananan hukumomi 44 domin a yi zabe lafiya a tashi lafiya yau Asabar.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta tsige ƴan takarar ciyaman 44 na jam'iyyar NNPP a zaben da ake shirin yi idan Allah ya kaimu gobe Asabar a jihar.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ƙaryata rade-radin da ake cewa ya nemi wa'adi na uku a karshen mulkinsa inda ya ce da yana so da ya yi.
A yan kwanakin nan, an hango daya daga jagororin a waren kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya mika wasika kasar Birtaniya ya na neman goyon baya kan samar da kasarsu.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar za ta karbe jihar Rivers. Ganduje ya je jihar Rivers ta APC ce.
Masu ruwa da tsaki na PDP a shiyyar Arewa ta Tsakiya sun fara zaman tattaunawa domin lalubo wanda za su gabatar a matsayin wanda zai maye gurbin Damagum.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Bola Tinubu ya yi la'akari da ra'ayoyin ƴan Najeriya wajen yanke ministocin za a kora, ta faɗi tsarin da aka bi wajen tantancewa.
Siyasar Najeriya
Samu kari