Siyasar Najeriya
Shigar Nasir El-Rufa'i ya fara jawo rudani a siyasar kasar nan. APC ta zargi El-Rufa'i da juwa baya saboda rasa mukami. Jam'iyyar PDP ta ce tana maraba da El-Rufa'i.
Tsohon shugaban kasan Najeriya, IBB ya bayyana dalilin da yasa ya kara Babangida a sunansa, saboda ana yi masa kallon Ba-Yarbe. Ya bayyana abin da ke ransa.
MURIC ta bayyana rashin jin dadi kan yadda tsohon shugaban kasa IBB ya bayyana cewa ba laifinsa bane rushe zaben 1993 da Abiola ya lashe a shekarar.
An ta hasashen ficewarsa daga APC, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya sake yin magana kan zaben 2027 da kuma hanyar ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Yayin da ake ta hasashen hadakar jam'iyyun adawa, Nasir El-Rufai, ya gana da shugabannin PDP a sirrance, abin da ya tayar da jita-jitar ficewarsa daga APC.
Jam'iyyun adawa sun bayyana cewa suna shiri na musamman domin tunkarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. Sun ce dole sai sun hadu kafin samun nasara.
Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana cewa babu wani ubangidanda da yake juya shi yadda yake so, ya ce waɗanda ake alaƙanta da shi su taimakonsa suka yi.
Jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana da ƙwarin guiwar cewa jam'iyyarsa ce za ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jam'iyyar LP na ci gaba da rasa jiga-jiganta ga APC da PDP, ciki har da Valentine Ozigbo, dan takarar gwamna, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a Anambra.
Siyasar Najeriya
Samu kari