Siyasar Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa kuma ɗaya daga cikin jagororin haɗaka, Salihu Lukman ya ce Obi ko Atiku, duk wanda ya samu nasara za a mara masa baya.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya yi magana kan shiga hadakar 'yan adawa. Ya ce da yawa daga cikinsu sun cutar da Najeriya.
Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu a majalisar dattawa, Abba Moro, ya bayyana cewa zai ci gaba da zama daram a jam'iyyar PDP. Ya yi watsi da batun shiga hadaka.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Bababchir Lawal ya ce wasu manyan 'yan APC da gwamnoni na goyon bayan hadakar APC a boye domin kifar da Tinubu.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya bayyana cewa lokacin yaudarar ƴan Najeriya ya wuce, ya kamata haɗakar yan adawa su yi bayani kan tallafin fetur.
Peter Obi ya wanke kan shi daga zargin da aka masa kan cewa ya hada kai da Janar Sani Abacha wajen yin badakala. Obi ya ce kasuwanci ne ya hada su da Abacha.
Kungiyar magoya bayan APC a Arewacin Najeriya suj bayyana Mohammad Kailani a matsayin wanda ya dace ya karɓi shugabancin jam'iyya a matakin ƙasa.
An yi taron hadakar 'yan adawa karkashin ADC a jihar Gombe. 'Yan siyasa a PDP da APC sun shiga tafiyar hadaka a yayin taron da ADC ta ce ta shirya kayar da APC.
Ƴan takarar gwamna 2 a Ondo, Eyitayo Jegede, Agboola Ajayi da wasu jiga-jigan PDP sun koma ADC, inda suka shiga haɗakarsu Atiku domin kalubalantar APC a zaɓen 2027.
Siyasar Najeriya
Samu kari