Siyasar Najeriya
Tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya ce ba zai shiga hadakar siyasa ba saboda rashin gaskiya da cike da ruɗani da kuma don kai.
Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ireti Kingibe ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar LP zuwa ADC ta 'yan hadaka.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya sake bayyana aniyarsa ta gwada sa'arsa wajen neman shugabancin Najeriya a 2027.
Shugaban malaman Izala na kasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi huduba mai zafi kan Yusuf Sambo Rigachikun kan tarbar Peter Obi da ya yi a jihar Kaduna.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya aika da sakon gargadi ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan zaben 2027 da ake tunkara.
Jam'uyyar haɗaka watau ADC na ci gaba da shirye shiryen shirya sahihin zaɓen fidda gwani, Atiku, Obi da Amaechi za su rattaɓa hannu kan yarjejeniya.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya fadi matakin da zai ɗauka kan gwamnatin Godwin Obaseki da ta shude bayan samun nasara a kotun koli kan zargin badakalar kudi.
Tsagin jam'iyyar NNPP ta gaza samun damar shiga zaben kananan hukumomi da ake a jihar Legas. Tsagin NNPP ya ce jinkirin INEC ma ya jawo mata rashin shiga zaben.
Tsohon sanata daga Ekiti, Mista Ojudu ya bayyana cewa abin da matukar mamaki da al'ajabi yadda Ganduje ya dawo siyasa ƙasa da mako 2 bayan ya ce ba shi da lafiya.
Siyasar Najeriya
Samu kari