Siyasar Najeriya
Tsakanin Janairu da Maris din 2025, Najeriya ta fuskanci gagarumin sauyin jam’iyyu da ya shafi manyan 'yan siyasa, ciki har da Mallam Nasir El-Rufai.
Tsohon sanatan Bauchi, Suleiman Nazif ya fice daga PDP zuwa SDP don samar da shugabanci na gari. Ya ce matakin ya biyo bayan shawarwari da amincewar mabiyansa.
Shugaban NNPP na jihar Ondo, Peter Olagookun ya bukaci Atiku Abubakar da sauran ƴan adawa su marawa Rabiu Musa Kwankwaso baya a zaɓen 2027 mai zuwa.
Jam'iyyun siyasa da kungiyoyi sun fara magana kan neman hana Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi takara a 2027. Kudirin ya kayyadae shekarun takara zuwa 60.
Atiku ya musanta karbar kudi daga Sanwo-Olu, yana mai cewa zargin karya ne. Tawagarsa ta bukaci EFCC ta bayyana bincikenta, domin dakile makircin 'yan siyasa.
Mai martaba sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gmabari ya bukaci ƴan siyasa su zama mutane masu faɗin gaskiya komai ɗacinta, sun daina yi wa mutane ƙarya.
Kungiyar IYC ta duniya ta kalubalanci shugaban riko na jihar Ribas bayan ya sanar da dakatar da jami'an gwamnati da gwamna Siminalayi Fubara ya nada.
Tsofaffin ƴan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PRP sun bi sahun tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun koma SDP domin ceto Najeriya.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya zabi wanda zai gaje shi a matsayin gwamna a zaben shekarar 2027.
Siyasar Najeriya
Samu kari