Siyasar Najeriya
Ministan gidaje da ci gaban birane, Ahmed Dangiwa, ya bayyana cewa ya gamsu da kamun ludayin mulkin Gwamna Dikko Radda na Katsina. Ya ce ya cancanci komawa kujerar.
Mataimakin shugaban SDP na Kudu maso Gabas, Sir. Arinze Ekelem ya buƙaci manyan ƴan adawa da jiga-jigan jam'iyya mai mulki su shigo jam'iyya don ceto Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya fito ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya fice daga jam'iyyar.
SDP ta gargadi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da sababbin mambobi su bi dokokin jam’iyya, su guji yunkurin rushe shugabanci ko sauya tsarin jam’iyyar.
Kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta yanke hukuncin sauke Juliis Abure daga shugabancin jam'iyyar LP na ƙasa, ta ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure.
Akpabio ya musanta zargin Abbo na korar sanatoci 5 daga majalisa. Ya bayyana cewa zai ci gaba da shugabanci mai ma’ana don ci gaban kasa da gina dimokuradiyya.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta watau INEC ta sanar da shugaban Majalisar Dattawa, Godwill Akpabio cewa ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha Akpotu kiranye.
Yayin da ƴan adawa ke shirye shiryen haɗewa domin kayar da Bola Tinubu, wata kungiyar siyasa ta nemi hukumar zaɓe INEC ta yi mata rijistar zama jam'iyyar siyasa.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kuros Riba ta bayyana cewa ta cimma matsayar ba Gwamna Bassey Otu tikicin neman tazarce a kujerarsa a babban zaɓen 2027.
Siyasar Najeriya
Samu kari