Siyasar Najeriya
Shugaban rikon jihar Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas ya nada shugabannin riko a kananan hukumomi 23 duk da kotu ta hana shi. Kotu ta hana shi cigaba da yin nade nade.
Yayin da ƴan adawa ke shirye-shiryen haɗaka domin tunkarar APC a zaɓen 2027, ɗan majalisar dokokin Enugu, Eze Gabriel ya sauya shwka daga LP zuwa PDP.
Kungiyar AEISCID ta bukaci a tsige Sanata Onyekachi Nwebonyi saboda kalamansa marasa dacewa kan rikicin Natasha da Akpabio da kare wanda ake zargi.
Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ya gana da 'yan majalisar da aka dakatar a Rivers. Hakan na zuwa ne bayan an dakatar da gwamna Simi Fubara da mataimakiyarsa.
'Yan ta’adda sun farmaki ofishin jam'iyyar LP a Legas, inda suka sace muhimman kayayyaki da makudan kudade. LP dai ta zargi Gwamna Otti da cin amanar jam’iyya.
Yayin da ake ta mamakin shiru da Sanata Bukola Saraki ya yi, wasu sun ce yana yin haka ne da nufin tsara matakin da zai fi amfani a siyasarsa kafin 2027.
Wani matashi, Ibrahim Modibbo ya ce Tinubu bai ci jiharsa ba a 2023, Arewa ta taimaka masa, amma yanzu tana shan wahala. Ya nemi Arewa da Kudu so kada Tinubu a 2027.
Bangaren Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da batun da kw nuna cewa Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta kwace shugabancin jam'iyyar NNPP daga hannunsa.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana jam'iyyar APC ta lallaba shi domin ya yi takarar sanatan Edo ta Tsakiya a babban zaben shekarar 2023.
Siyasar Najeriya
Samu kari