Siyasar Najeriya
Bayan saba umarninta, wata kotun tarayya da ke Port Harcourt ta bukaci shugaban mulkin jihar Ribas ya bayyana dalilin da yasa ya nada shugabannin kananan hukumomi.
Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ya bar mulki da dukiyar da ya mallaka tun kafin ya zama shugaban kasa ba tare da ta ƙaru ba.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa bai tattauna da kowa ba kan batun ficewa daga jam'iyyar. Ya ce yana na daram.
Prince Adebayo ya ce Tinubu yana aikata abubuwan da za su jawo jam'iyyar APC ta fadi zaben 2027, inda ya ce yana da yakinin SDP ce al'umma za su zaba.
Kotun daukaka kara ta bayyana cewa nan gaba kadan za ta aika da ranar sanar da hukuncin da ta yanke a kan dambarwar zaben kananan hukumomi a jihar Kano.
Shugaban rikon jihar Rivers, Ibok-Ete Ekwe Ibas ya nada shugabannin riko a kananan hukumomi 23 duk da kotu ta hana shi. Kotu ta hana shi cigaba da yin nade nade.
Yayin da ƴan adawa ke shirye-shiryen haɗaka domin tunkarar APC a zaɓen 2027, ɗan majalisar dokokin Enugu, Eze Gabriel ya sauya shwka daga LP zuwa PDP.
Kungiyar AEISCID ta bukaci a tsige Sanata Onyekachi Nwebonyi saboda kalamansa marasa dacewa kan rikicin Natasha da Akpabio da kare wanda ake zargi.
Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ya gana da 'yan majalisar da aka dakatar a Rivers. Hakan na zuwa ne bayan an dakatar da gwamna Simi Fubara da mataimakiyarsa.
Siyasar Najeriya
Samu kari