Siyasar Najeriya
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ayyana Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin jagoran jam’iyyar a Jihar Rivers bayan ya sauya sheka.
Rigimar siyasa a jihar Kano na kara dauki dumi bayan Gwamna Baba ya shirya komawa APC, bayanai sun nuna Kwankwaso na duba yiwuwar komawa jam'iyyar ADC.
Jam'iyyar PDP reshen jihar Plateau ta yi martani kan sauya shekar da Gwamna Caleb Mutfwang ya yi zuwa APC. Ta ce gwamnan ko kadan bai yi shawara da ita ba.
Gwamna Siminalayi Fubara ya fara fuskantar kalubalen bayan barin jam'iyyar PDP, ana zargin ya aaba yarjejeniyar sulhu da Tinubu ya yi masu a Aso Rock.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, da karya yarjejeniyar da Shugaba Bola Tinubu ya sasanta.
Jam'iyyar APC mai mulki ta ce Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2027. Ta yi martani ne bayan Peter Obi ya shiga ADC ya hade da Atiku Abubakar a karshen 2025.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi wa Peter Obi maraba zuwa jam'iyyar ADC. Ya ce shigowarsa na da muhimmanci ga adawa a Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC. Peter Obi ya ce suna da shirin ceto Najeriya.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta tanka bayan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba ta da matsguni a siyasar jihar Rivers.
Siyasar Najeriya
Samu kari