Siyasar Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bukaci Fulani su ɗauki batun zaman lafiya da muhimmanci, inda ya ce tarihi ya nuna ba su yarda da tashin tashina ba.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi yan APC da sauran jam'iyyu har 1776 zuwa NNPP a Kano. Hakan share hanya ne ga Abba Kabir Yusuf kan zaben gwamna na 2027.
Alamu sun nuna alaƙa ta fara tsami tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso, sun fara samun sabani kan kujerar SSG da kwamishinan yaɗa labarai.
Rikici ya kara kunno kai a jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano yayin da aka samu bayyanar sabon shugaba a cikinta, an samu bullar sabon shugaba a cikinta.
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai ce komai ba dangane da rigimar cikin gida da ta ɓarke a jam'iyyar NNPP ta jihar Kano.
Abba Kabir Yusuf ya kashe wutar rikici tsakanin Abdullahi Baffa Bichi da jiga jigan yan NNPP a Kano. Abba ya yi sulhu a tsakaninsu ne a fadar gwamnatin jihar Kano.
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya musanta alaka da kungiyar da ake zargin yana daukar nauyinta ta 'Abba tsaya da kafarka' a Kano.
Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta kara faɗawa cikin rikici da aka ji sanarwar dakatar da sakataren gwamnati, Baffa Bichi da kwamishinan sufuri.
Yusuf Kibiya ya samu goyon bayan mafi yawan jagororin jam'iyyar PDP a jihar Kano, inda ya samu nasara a kan abokan takararsa da suka hada da Nura Nuhu da Sani Aliyu.
Siyasar Kano
Samu kari