Gwamna Abba Ya Shirya Ɗaukar Sababbin Ma'aikata Sama da 17,000 a Kano, Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gama shirye-shiryen ɗaukar jami'an tsaro 17,600 a jihar
- Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatn za ta ɗauki mafarauta aikin tsaro a wani ɓangare na kokarin bunƙasa harkokin ilimi
- Jami'an tsaron da gwamnatin ke shirin ɗauka za su yi aikin gadin makarantun gwamnati a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa tuni ta gama shirye-shiryen fara ɗaukar ma'aikatan tsaro da mafarauta 17,600.
Bayanai sun nuna cewa gwamnatin za ta ɗauki jami'an tsaron ne domin gadin makarantun gwamnati a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Mai taimakawa gwamna kan harkokin digital midiya, Abdullahi Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarws da ya wallafa a shafin X ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano za ta ɗauki mutum 17,000 aiki
Kwamishinan ilimi, Umar Doguwa ne ya sanar da haka a lokacin da ya karɓi bakuncin kungiyar tsofaffin ɗaliban Rumfa da suka kai masa ziyara a ofis.
Ya ce akwai buƙatar gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da ɗaiɗaikun mutane su haɗa karfi da karfe idan ana son magance ƙalubalen da suka baibaye harkar ilimi.
Kwamishinan wanda ya samu wakilcin babbar sakatariyar ma'aikatan ilimi ta Kano, Kubra Imam ya ce a shirye suke su yi aiki da ƙungiyoyi don gyara ilimi.
Gwamnatin Kano na kokarin gyara harkar ilimi
A cewarsa, matakin da gwamnatin Abba ta ɗauka na ayyana ta ɓace a harkar ilimin Kano ya nuna shirinta na warware matsalolin da suka taɗiye ɓangaren.
Umar Soguwa kuma yi nuni da cewa, domin cimma wannan manufa, gwamnati za ta ci gaba da hada kai da tsofaffin dalibai da sauran kungiyoyi masu zaman kansu domin aiwatar da karin shirye-shirye na bunkasa ilimi a jihar.
Gwamnan Kano ya bada tallafin N100m a Jigawa
A wani rahoton kuma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya zama gwamna na farko da ya taka kafa a jihar Jigawa domin ba da tallafi da jajen fashewar tanka.
Abba Kabir Yusuf ya gana da gwamna Umar Namadi a fadar gwamnatin Jigawa, ya yi jaje ga waɗanda hadarin fetur ya shafa, sanna ya ba da tallafin N100m.
Asali: Legit.ng