Siyasar Kano
Bayan dawowa daga Abuja ana cikin rikicin siyasa, Abba Kabir Yusuf ya yi zaman majalisar zartarwa. Za a ji ayyukan da aka amince da su a jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta bayyana shirinta na ɗaukar jami'an tsaro musamman mafarauta aikin gadin makarantu gwamnati a faɗin kananam hukumomi 44 a jihar.
'Yan Kano sun rike mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin ‘yan majalisar wakilan tarayya. A 2023 Bashir Lado kuma ya samu makamancin wannan matsayi.
Wasu jiga jigan jam'iyyar NNPP a Kano da suka hada da Alhaji Auwalu Yusuf Dawakin Tofa sun sauya sheka zuwa APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce abubuwa da ke faruwa a NNPP ya kara nuna gaskiyar maganar da yake faɗa kan Kwankwaso, ya buƙaci Abba Kabir ya canza tunani.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bukaci Fulani su ɗauki batun zaman lafiya da muhimmanci, inda ya ce tarihi ya nuna ba su yarda da tashin tashina ba.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi yan APC da sauran jam'iyyu har 1776 zuwa NNPP a Kano. Hakan share hanya ne ga Abba Kabir Yusuf kan zaben gwamna na 2027.
Alamu sun nuna alaƙa ta fara tsami tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso, sun fara samun sabani kan kujerar SSG da kwamishinan yaɗa labarai.
Rikici ya kara kunno kai a jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano yayin da aka samu bayyanar sabon shugaba a cikinta, an samu bullar sabon shugaba a cikinta.
Siyasar Kano
Samu kari