Siyasar Kano
Gwamnatin jihar Kano ta musanta alakar siyasa da kuma sauye-sauyen manyan sakatarori a ma'aikatu da aka yiwa wasu manyan daraktoci da cewa rigimar NNPP ta jawo.
Jarumar Kannywood kuma hadimar gwamnan jihar Kano, Asma'u Abdullahi, ya fice daga jam'iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya. Asma'u ta koma jam'iyyar APC.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki zafi kan masu kiran ya tsaya da kafarsa, ya ce wannan babban cin mutunci ne saboda ana nufin bai ma san abinda yake ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa alakarsa da Kwankwaso ta yi tsami har ya daina ɗaga kiran wayarsa, ya ce wannan karya ne.
Lauyan yaran nan 73 da gwamnatin Tinubu ta cafke daga Kano bisa zargin yunkurin kifar da ita, Barista Hamza Nuhu Dantani ya bayyana yadda gwamnan ya kawo masu agaji
Rahotanni sun bayyana cewa wasu kusoshin jam'iyyar NNPP a Kano sun fara nuna shakku kan shugabancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya.
Dan majalisar tarayya mai wakilar karamar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini ya yi tonon silili kan barakar da ake zargin ta bulla tsakanin Kwankwaso da gwamna Abba
Shugaban kungiyar Kwankwasiyya a Kano, Musa Gambo Hamisu ta yi martini kan ficewa da wasu jiga-jigan NNPP su ka ce sun yi daga tafiyar saboda wasu dalilai,
Majalisar dokokin jihar Kano ta yi bayani kan samuwar yan bangaren Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf a majalisa. Ya ce ba ruwansu da zancen Abba tsaya da kafarka.
Siyasar Kano
Samu kari